Littafi Mai Tsarki

L. Fir 8:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Musa,

2. “Ɗauki Haruna da 'ya'yansa maza, da rigunan, da man keɓewa, da bijimi na yin hadaya don zunubi, da raguna biyu, da kwandon abinci marar yisti.

3. Ka kuma tattara jama'a duka a ƙofar alfarwa ta sujada.”