Littafi Mai Tsarki

L. Fir 7:21-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a raba wannan mutum da mutanensa.

22. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

23. ya faɗa wa mutanen Isra'ila cewa, kada su ci kitsen sa, ko na tunkiya, ko na akuya.

24. Kitsen dabbar da ta mutu mushe, da kitsen dabbar da namomin jeji suka yayyaga, za a iya yin wani amfani da shi, amma kada a kuskura a ci.

25. Duk mutumin da ya ci kitsen dabbar da aka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, za a raba shi da mutanensa.

26. Ko kaɗan, ba za a yi abinci da jini ba, ko na tsuntsu, ko na dabba, a inda suke duka.

27. Duk mutumin da ya karya wannan doka za a raba shi da mutanensa.

28. Ubangiji kuma ya ba Musa waɗannan ka'idodi

29. don mutanen Isra'ila, cewa, wanda zai miƙa hadayarsa ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama.

30. Sai shi kansa ya kawo hadayar da za a ƙona. Zai kawo kitsen da ƙirjin. Za a yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin a gaban Ubangiji.

31. Firist zai ƙone kitsen a bisa bagaden, amma ƙirjin zai zama rabon Haruna da 'ya'yansa maza.

32. Za a ba firist cinya ta dama, don hadaya ta ɗagawa daga cikin hadayu na salama.

33. Cinyar ƙafar dama za ta zama rabon ɗan Haruna wanda ya miƙa jinin da kitsen hadaya ta salama.

34. Gama Ubangiji ya ba Haruna da 'ya'yansa maza, ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka ɗaga, su zama rabonsu daga cikin hadayu na salama na Isra'ilawa. Ya ba Haruna, firist, da 'ya'yansa maza, su zama rabonsu har abada daga cikin hadayu na Isra'ilawa.

35. Wannan shi ne rabon da aka keɓe wa Haruna da 'ya'yansa maza, daga cikin hadayun da ake yi da wuta ga Ubangiji, tun a ranar da aka keɓe su firistoci na Ubangiji.