Littafi Mai Tsarki

L. Fir 7:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗannan su ne ka'idodin hadaya don ramuwa, hadaya ce tsattsarka.

2. Za a yanka dabbar hadayar a arewa da bagaden inda akan yanka hadaya don ƙonawa. Sai a yayyafa jinin a kan bagaden da kewayensa.

3. Za a miƙa kitsen abin hadaya duka, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki,