Littafi Mai Tsarki

L. Fir 7:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗannan su ne ka'idodin hadaya don ramuwa, hadaya ce tsattsarka.

2. Za a yanka dabbar hadayar a arewa da bagaden inda akan yanka hadaya don ƙonawa. Sai a yayyafa jinin a kan bagaden da kewayensa.