Littafi Mai Tsarki

L. Fir 25:42-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

42. Gama su bayina ne, waɗanda na fanshe su daga ƙasar Masar, ba za a sayar da su kamar yadda ake sayar da bayi ba.

43. Kada ka mallake shi da tsanani, amma ka ji tsoron Allahnka.

44. Amma a kan bayi mata da maza da kuke so ku samu, kwa iya sayensu daga al'ummar da yake kewaye da ku.

45. Kwa iya sayen bayi daga baƙin da yake baƙunci a wurinku, su da iyalinsu waɗanda aka haifa a ƙasarku. Kwa iya sayensu su zama dukiyarku.

46. Kwa iya barinsu ga 'ya'yanku maza a bayanku su gāda, su zama abin mallakarsu har abada. Kwa iya bautar da su, amma 'yan'uwanku, Isra'ilawa, ba za ku mallaki juna da tsanani ba.

47. “Idan baƙo ne ko mai aikin ijara da yake zaune tare da ku ya arzuta, ɗan'uwanku kuwa wanda yake kusa da shi ya talauce, har ya sayar da kansa ga baƙon, ko mai aikin ijarar da yake tare da ku, ko kuwa ga wani daga cikin iyalin baƙon,

48. bayan da ya sayar da kansa ana iya fansarsa. Wani daga cikin 'yan'uwansa ya iya fansarsa.

49. Ko kawunsa, ko ɗan kawunsa, ko wani daga cikin danginsa na kusa ya iya fansarsa. Idan kuma shi kansa ya arzuta ya iya fansar kansa.