Littafi Mai Tsarki

L. Fir 25:40-55 Littafi Mai Tsarki (HAU)

40. Amma ya zauna tare da kai kamar bara na ijara, ko kuwa kamar wanda yake baƙunci. Sai ya yi aiki tare da kai har shekara ta hamsin ta murna ta kewayo.

41. Sa'an nan shi da iyalinsa su rabu da kai, ya koma wurin danginsa da mahallin kakanninsa.

42. Gama su bayina ne, waɗanda na fanshe su daga ƙasar Masar, ba za a sayar da su kamar yadda ake sayar da bayi ba.

43. Kada ka mallake shi da tsanani, amma ka ji tsoron Allahnka.

44. Amma a kan bayi mata da maza da kuke so ku samu, kwa iya sayensu daga al'ummar da yake kewaye da ku.

45. Kwa iya sayen bayi daga baƙin da yake baƙunci a wurinku, su da iyalinsu waɗanda aka haifa a ƙasarku. Kwa iya sayensu su zama dukiyarku.

46. Kwa iya barinsu ga 'ya'yanku maza a bayanku su gāda, su zama abin mallakarsu har abada. Kwa iya bautar da su, amma 'yan'uwanku, Isra'ilawa, ba za ku mallaki juna da tsanani ba.

47. “Idan baƙo ne ko mai aikin ijara da yake zaune tare da ku ya arzuta, ɗan'uwanku kuwa wanda yake kusa da shi ya talauce, har ya sayar da kansa ga baƙon, ko mai aikin ijarar da yake tare da ku, ko kuwa ga wani daga cikin iyalin baƙon,

48. bayan da ya sayar da kansa ana iya fansarsa. Wani daga cikin 'yan'uwansa ya iya fansarsa.

49. Ko kawunsa, ko ɗan kawunsa, ko wani daga cikin danginsa na kusa ya iya fansarsa. Idan kuma shi kansa ya arzuta ya iya fansar kansa.

50. Sai ya sa wanda ya saye shi ya lasafta tun daga shekarar da ya sayar da kansa, har zuwa shekara ta hamsin ta murna. Ƙuɗin da za a fanshe shi zai zama daidai da yawan shekarun da suka ragu kafin shekara ta murna. Sai a ɗauke shi kamar bara na ijara.

51. Idan shekarun sun ragu da yawa, sai ya fanshi kansa bisa ga adadin kuɗin da aka saye shi.

52. Amma idan shekarun sun ragu kaɗan kafin shekara ta hamsin ta murna, sai ya lasafta, ya biya don fansarsa bisa ga yawan shekarun.

53. Sai baƙon ya mai da shi kamar bara mai aikin ijara, shekara a kan shekara. Amma kada ya tsananta masa.

54. Idan ba a fanshe shi ta waɗannan hanyoyi ba, sai a shekara ta hamsin ta murna, a sake shi, shi da 'ya'yansa.

55. Gama a gare ni Isra'ilawa bayi ne waɗanda na fisshe su daga ƙasar Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.”