Littafi Mai Tsarki

L. Fir 22:22-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko mai gundumi, ko mai ɗiga, ko mai susa, ko mai kirci, kada ku miƙa wa Ubangiji, kada kuma ku yi hadaya ta ƙonawa a bagaden Ubangiji da su.

23. Kwa iya ba da dabba, marar cikakkiyar halitta don hadaya ta yardar rai, amma ba za ku bayar don hadaya ta cika wa'adi ba, ba za a karɓa ba.

24. Kowace dabba kuma da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa, ba za ku miƙa ta hadaya ga Ubangiji ba, ba kuwa za ku yi hadaya da ita a ƙasarku ba.

25. “Ba kuma za ku karɓi irin dabbobin nan daga hannun baƙo don ku miƙa su hadaya ga Ubangiji ba, marasa tsarki ne tun da yake suna da lahani, ba za a karɓa ba.”

26. Ubangiji ya yi magana da Musa, ya ce,

27. “Sa'ad da kuma aka haifi ɗan maraƙi, ko ɗan rago, ko ɗan akuya, zai yi kwana bakwai tare da uwarsa. A rana ta takwas zuwa gaba, sai a karɓe shi don yin hadaya ta ƙonewa ga Ubangiji.

28. Ba za ku yanka uwar dabbar tare da ɗanta rana ɗaya ba, ko uwar saniya ce, ko ta tunkiya ce.

29. Sa'ad da za ku miƙa hadaya ta godiya ga Ubangiji, sai ku miƙa ta yadda za a karɓa.

30. A ranar ce za a cinye, kada a bar kome ya kai gobe. Ni ne Ubangiji.

31. “Ku yi biyayya da umarnina. Ni ne Ubangiji.

32. Kada ku jawo wa sunana mai tsarki ƙasƙanci, amma sai mutanen Isra'ila su gane, ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji na kuwa tsarkake ku,

33. na kuma fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji.”