Littafi Mai Tsarki

L. Fir 20:12-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Duk wanda ya kwana da matar ɗansa, za a kashe su duka biyu ɗin, gama sun yi abin da yake haram. Alhakin jininsu yana wuyansu.

13. Duk mutumin da ya kwana da namiji kamar yadda namiji yake kwana da mace, su biyu ɗin, sun yi aikin ƙazanta, za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu.

14. Duk mutumin da ya auri 'ya tare da mahaifiyarta, wannan mugun abu ne, shi da su biyu ɗin, sai a ƙone su da wuta, don kada mugun abu ya kasance a cikinku.

15. Idan mutum ya kwana da dabba, sai a kashe shi, a kuma kashe dabbar.

16. In kuma mace ta yi ƙoƙari har ta kwana da dabba, sai a kashe matar tare da dabbar, alhakin jininsu yana wuyansu.

17. “Idan mutum ya auri ƙanwarsa ko kuma 'yar mahaifinsa, sai a ƙasƙantar da su a bainar jama'a, a kuwa kore su daga cikin jama'a. Ya kwana da ƙanwarsa ke nan, tilas su sha hukuncin laifinsu.

18. Idan mutum ya kwana da mace a lokacin hailarta, duka biyunsu za a kore su daga cikin jama'arsu, gama sun karya ka'idodi a kan rashi tsarki.

19. “Idan mutum ya kwana da bābarsa ko innarsa, za a hukunta duka biyunsu saboda abin ƙyama da suka yi.

20. Idan kuma mutum ya kwana da matar kawunsa, ya ƙasƙantar da kawunsa, sai su ɗauki alhakin laifinsu, za su mutu ba haihuwa.

21. Idan mutum ya auri matar ɗan'uwansa, ya yi mugun abu, za su mutu ba haihuwa, gama ya ƙasƙantar da ɗan'uwansa.