Littafi Mai Tsarki

L. Fir 19:4-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. “Kada ku juya ku bi gumaka, ko kuma ku yi wa kanku gumaka na zubi. Ni ne Ubangiji Allahnku.

5. “Sa'ad da za ku miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta domin a karɓe ku.

6. A cinye ta a ranar da kuka miƙa ta ko kuwa kashegari. Abin da ya ragu har kwana na uku, sai a ƙone da wuta,