Littafi Mai Tsarki

L. Fir 18:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Kada ya kwana da 'yar matar mahaifinsa, wadda mahaifinsa ya haifa, tun da yake ita 'yar'uwarsa ce.

12. Kada ya kwana da bābarsa gama 'yar'uwar mahaifinsa ce.

13. Kada ya kwana da innarsa, gama ita 'yar'uwar mahaifiyarsa ce.

14. Kada ya kwana da matar ɗan'uwan mahaifinsa, gama ita ma bābarsa ce.

15. Kada ya kwana da matar ɗansa, gama ita surukarsa ce.

16. Kada ya kwana da matar ɗan'uwansa, gama ita matar ɗan'uwansa ce.

17. In ya kwana da mace, kada kuma ya kwana da 'yarta, ko jikanyarta, wannan duk haramun ne, gama su danginsa ne na kusa.

18. Muddin matarsa tana da rai, ba zai auro ƙanwarta ta zama kishiyarta ba.