Littafi Mai Tsarki

L. Fir 15:14-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. A kan rana ta takwas zai kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada, ya ba firist.

15. Sai firist ya yi hadaya da su, ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist ɗin zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji domin ɗigarsa.

16. Idan maniyyin mutum ya zubo, sai ya wanke jikinsa duka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

17. Kowace riga ko fatar da maniyyin ya taɓa, sai a wanke da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

18. Idan mutum ya kwana da mace, sai su yi wanka da ruwa, sun ƙazantu har maraice.

19. Sa'ad da mace take haila irin ta ka'ida, za ta ƙazantu har kwana bakwai, duk wanda ya taɓa ta kuwa zai ƙazantu har maraice.

20. Duk abin da ta kwana a kai a lokacin rashin tsarkinta zai ƙazantu, haka kuma abin da ta zauna a kai zai ƙazantu.

21. Wanda kuma ya taɓa gadonta, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

22. Haka kuma duk wanda ya taɓa kowane abin da ta zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

23. Ko gado ne, ko kuma kowane abin da ta zauna a kai, sa'ad da wani ya taɓa shi zai ƙazantu har maraice.

24. Idan kuma wani ya kwana da ita, rashin tsarkinta zai shafe shi. Zai zama marar tsarki har kwana bakwai. Kowane gado da ya kwanta a kai zai ƙazantu.

25. Idan zubar jinin hailar macen ya yi kwanaki da yawa, ko kuwa kwanakin hailarta sun zarce ka'ida, a duk kwanakin zubar jininta za ta lizima cikin rashin tsarki daidai kamar lokacin hailarta.