Littafi Mai Tsarki

L. Fir 13:41-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

41. Idan gashin goshin mutum ya zube, ya yi sanƙo ke nan, amma shi tsattsarka ne.

42. Idan a sanƙon ko a gaban goshi akwai tabon cuta jaja-jaja da fari-fari, to, kuturta ce ta faso a sanƙonsa ko gaban goshinsa.

43. Firist kuwa zai dudduba shi, idan an ga kumburin jaja-jaja da fari-fari ne a sanƙon kansa, ko a gabansa kamar alamar kuturta a fata jikinsa,

44. to, kuturu ne shi, marar tsarki. Firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta tana kansa.

45. Mai kuturta zai sa yagaggun tufafinsa, ya bar gashin kansa ba gyara, sa'an nan ya rufe leɓensa na sama, ya ta da murya, ya riƙa cewa, “Marar tsarki, marar tsarki.”

46. Muddin yana da cutar, zai zama marar tsarki. Zai zauna shi kaɗai a bayan zango.

47. Idan ana tsammani akwai cutar kuturta a rigar ulu ko ta lilin,

48. ko a tariyar zaren, ko a waɗari, ko a lilin, ko a ulu, ko a cikin fata, ko cikin kowane abu da aka yi da fata,

49. idan cutar ta zama kore-kore, ko jaja-jaja a rigar, ko a fatar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, wannan cuta kuturta ce, sai a nuna wa firist.