Littafi Mai Tsarki

L. Fir 11:41-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

41. Ba za ku ci ƙananan dabbobin da suke motsi a bisa ƙasa ba,

42. duk waɗanda suke jan ciki, da waɗanda suke da ƙafa huɗu, da waɗanda suke da ƙafafu da yawa.

43. Kada ku ƙazantar da kanku da cin waɗannan abubuwa.

44. Ni ne Ubangiji Allahnku, domin haka dole ku tsarkake kanku, ku tsarkaka, gama ni mai tsarki ne.