Littafi Mai Tsarki

K. Mag 7:6-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Wata rana ina leƙawa ta tagar ɗakina,

7. sai na ga waɗansu samari masu yawa waɗanda ba su gogu da duniya ba, musamman sai na lura da wani dolo a cikinsu.

8. Yana tafe a kan titi kusa da kusurwar da take a zaune, yana wucewa kusa da gidanta,

9. da magariba cikin duhu.

10. Sai ta tarye shi, ta ci ado kamar karuwa, tana shirya yadda za ta yaudare shi.

11. (Ba ta jin tsoro, ba ta kuma jin kunya, ko yaushe tana ta gantali a tituna.

12. Takan tsaya tana jira a kowace kusurwa, wani lokaci a tituna, wani lokaci kuma a kasuwa.)

13. Ta rungumi saurayin, ta sumbace shi, ta dubi tsabar idonsa ta ce,

14. “Na miƙa hadayu yau, ina da nama na hadayu.

15. Shi ya sa na fito ina nemanka, ina so in gan ka, ga shi kuwa, na gan ka!

16. Na lulluɓe gadona da zannuwan lilin masu launi iri iri daga Masar.

17. Na yayyafa musu turaren mur da na aloyes da na kirfa.

18. Ka zo mu sha daɗin ƙauna, mu more dukan dare, mu yi farin ciki rungume da juna.