Littafi Mai Tsarki

K. Mag 6:33-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Zai sha dūka, a wulakanta shi, zai dawwama cikin kunya.

34. Hasalar miji mai kishi babu irinta, ramawarsa ba dama.

35. Ba zai karɓi biya ba, ba kyautar da za a yi masa wadda za ta kwantar da fushinsa.