Littafi Mai Tsarki

K. Mag 29:10-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Mutane masu kisankai suna ƙin amintaccen mutum, amma adalai za su kiyaye ransa.

11. Wawa yakan nuna fushinsa ko yaushe, amma mutum mai hikima yakan kanne fushinsa.

12. Idan mai mulki yana kasa kunne ga maganganun ƙarya, dukan ma'aikatansa za su zama maƙaryata.

13. Matalauci da azzalumi suna tarayya a abu ɗaya, wato dukansu Ubangiji ne yake ba su ganin gari.

14. Idan sarki yana yi wa talakawa shari'ar gaskiya, zai daɗe yana mulki.