Littafi Mai Tsarki

K. Mag 27:19-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Yadda kake ganin fuskarka a ruwa, haka kake ganin kanka a zuciyarka.

20. Muradin mutum kamar lahira yake, a kullum ba ya ƙoshi.

21. Da wuta ake gwada azurfa da zinariya, amma yabon da ake yi wa mutum shi ne magwajinsa.

22. Ko da za ka doki wawa ka bar shi tsakanin rai da mutuwa, duk da haka yana nan da wautarsa kamar yadda yake.

23. Ka lura da garkunan tumakinka da na shanunka da kyau iyakar iyawarka,

24. domin dukiya ba ta tabbata har abada, al'ummai ma haka ne.

25. Ka yanki ingirici, lokacin da yake toho kana iya yankar ciyawa a gefen tuddai.

26. Kana iya yin tufafi da ulun tumakinka, kana iya sayen gona da kuɗin awakinka.

27. Madarar awakinka za ta zama abincinka kai da iyalinka, da kuma barorinka 'yan mata.