Littafi Mai Tsarki

K. Mag 26:22-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Kamar yadda lomar abinci mai daɗi takan gangara can cikin ciki haka maganar mai gulma take.

23. Bakin da ba ya faɗar gaskiya, da zuciya mai ƙiyayya suna kama da kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba.

24. Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye ta da maganar bakinsa, yana kuma ƙunshe da munafunci.

25. Sa'ad da yake magana mai kyau kada ka gaskata shi, domin zuciyarsa tana cike da mugunta.

26. Ko da yake kila zai ɓoye ƙiyayyarsa, duk da haka muguntarsa za ta bayyana ga mutane.

27. Wanda ya haƙa ramin mugunta shi zai faɗa ciki, wanda kuma ya mirgino dutse, zai fāɗo a kansa.

28. Maƙaryaci yana ƙin wanda ya yi wa ƙarya, mai daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.