Littafi Mai Tsarki

K. Mag 25:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ga waɗansu sauran karin maganar Sulemanu waɗanda magatakardan Hezekiya Sarkin Yahuza suka juya.

2. Muna girmama Allah saboda abin da ya rufe, muna girmama sarakuna saboda abin da suka ba da bayaninsa.

3. Ba ku taɓa sanin abin da sarki yake tunani ba, gama tunaninsa sun fi ƙarfinmu. Kamar nisan sararin sama suke ko zurfafan teku.

4. Ka tace azurfa, gwani kuwa zai yi wani kyakkyawan abu da ita.

5. A kawar da mugayen mashawarta daga gaban sarki, hukumarsa za ta shahara a kan adalci.