Littafi Mai Tsarki

K. Mag 24:7-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Kalmomi masu hikima sun yi wa wawa zurfin ganewa ƙwarai, ba shi da ta cewa sa'ad da ake magana a kan muhimman abubuwa.

8. Idan a ko yaushe shirye-shiryen mugunta kake, za ka yi suna a kan kuta tashin hankali.

9. Kowace irin dabarar da wawa yake tunani a kanta zunubi ne. Jama'a suna ƙin mutum mai rainako.

10. Idan ba ka da ƙarfi a lokacin hargitsi, hakika ka tabbata marar ƙarfi.

11. Kada ka ji nauyin ceton wanda ake janye da shi zuwa inda za a kashe shi.

12. Mai yiwuwa ne ka ce kai ba ruwanka, amma Allah ya sani, yana kuwa auna manufofinka. Yana lura da kai, ya kuwa sani. Yakan sāka wa mutane a kan abin da suke aikatawa.

13. Ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau. Kamar yadda kakin zuma yake da zaƙi a harshenka,

14. haka ilimi da hikima suke da amfani ga ranka. Ka same su, a gaba za ka yi farin ciki.

15. Kada ka shirya dabarun yi wa amintacce ƙwace, ko ka ƙwace masa gidansa, wannan mugunta ce.

16. Ko sau nawa amintaccen mutum ya faɗi, ba abin damuwa ba ne, gama a ko yaushe zai sāke tashi, amma masifa takan hallaka mugaye.

17. Kada ka yi murna sa'ad da bala'i ya aukar wa maƙiyinka.

18. Ubangiji zai sani in kana murna, ba kuwa zai so haka ba, mai yiwuwa ne ba zai hukunta shi ba.

19. Kada ka damu saboda mugaye, kada ka yi ƙyashin masu aikata abin da ba daidai ba.