Littafi Mai Tsarki

K. Mag 24:28-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isasshen dalili ba, ko ka faɗi ƙarya a kansa.

29. Kada ka ce, “Zan yi masa daidai da yadda ya yi mini, zan rama masa!”

30. Na ratsa ta gonakin inabin wani malalaci, dakiki,

31. suna cike da ƙayayuwa, ciyayi sun sha kansu, katangar dutse da take kewaye da su ta faɗi.

32. Da na dubi wannan, na yi tunani a kansa, ya zamar mini ishara.

33. “Yi ta ruruminka, ci gaba da barcinka, rungume hannuwanka don ka shaƙata.”

34. Amma sa'ad da kake ta sharar barci fatara za ta auka maka kamar ƙungiyar 'yan fashi.