Littafi Mai Tsarki

K. Mag 24:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Kada ka ji ƙyashin mugaye, kada ka yi ƙoƙarin yin abuta da su.

2. Duk tunaninsu na yin mugunta ne, a duk lokacin da suka buɗe bakinsu sai sun cuci wani.

3. An gina gidaje a kan harsashin hikima da fahimi.