Littafi Mai Tsarki

K. Mag 23:4-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ka zama mai isasshiyar hikima, kada ka gajiyar da kanka garin ƙoƙarin neman dukiya.

5. Kuɗinka sun iya ƙarewa kamar ƙyiftawar ido, kamar suna da fikafikai su tashi kamar gaggafa.

6. Kada ka ci abincin marowaci, ko ka yi haɗamar kyakkyawan abincin da ya sa a gabanka.

7. Zai ce, “Bari a ƙara maka,” amma ba haka yake nufi ba. Kamar gashi yake a cikin maƙogwaronka.

8. Za ka harar da abin da ka ci, dukan daɗin bakinka zai tafi a banza.

9. Kada ka yi wa wawa magana irin ta haziƙai, gama ba zai yaba da maganarka ba.

10. Kada ka kuskura ka kawar da shaidar iyaka, ko ka ƙwace gonar marayu.

11. Ubangiji Mai Iko shi ne kāriyarsu, shi zai yi magana dominsu.

12. Ka mai da hankali ga malaminka, ka koyi dukan abin da kake iyawa.

13. Kada ka bar yaro ba horo, gama ko ka duke shi ba za a kashe shi ba.

14. Lalle ne za ka ceci ransa.

15. Ɗana, idan ka zama mai hikima zan yi murna ƙwarai.

16. Zan yi murna idan na ji kana faɗar magana da hikima.

17. Kada ka yi ƙyashin masu aikata zunubi tsoron Ubangiji kaɗai za ka sa a gaba.

18. Idan haka ta samu za ka yi farin ciki nan gaba.

19. Ka saurara, ya ɗana, ka zama mai hikima. Ka yi tunani mai zurfi a kan hanyarka.

20. Kada ka zauna da mashayan ruwan inabi, ko masu haɗama.

21. Gama bugaggu da ruwan inabi da masu zarin ci za su zama matalauta. Idan iyakar abin da kake yi daga ci sai barci ne, nan da nan za ka ga kana saye da tsummoki.

22. Ka kasa kunne ga mahaifinka, gama da ba dominsa ba, da ba ka, sa'ad da mahaifiyarka ta tsufa ka nuna mata godiyarka.