Littafi Mai Tsarki

K. Mag 23:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da ka zauna cin abinci tare da babban mutum, ka tuna da yadda yake.

2. Idan kai mai son ci da yawa ne sai ka kanne.

3. Kada ka yi haɗamar kyakkyawan abincin da yake gabanku, zai yiwu wayo yake so ya yi maka.

4. Ka zama mai isasshiyar hikima, kada ka gajiyar da kanka garin ƙoƙarin neman dukiya.