Littafi Mai Tsarki

K. Mag 20:4-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Manomin da ya cika lalaci, ya kasa nome gonakinsa a kan kari, a lokacin girbi ba zai sami kome ba.

5. Tunanin mutum kamar ruwa yake a rijiya mai zurfi, sai mai basira ya iya ya jawo shi.

6. Kowa gani yake shi mai biyayya ne, mai aminci. Amma ina? Ko ka yi ƙoƙari ka sami amintacce ɗaya daga cikinsu, ba za ka samu ba.

7. 'Ya'yan da mahaifinsu amintacce ne, wanda yake aikata abin da yake daidai, sun yi sa'a.

8. Sarkin da yake yin shari'a ta gaskiya, da ganin mugunta ya san ta.

9. Wane ne zai iya cewa lamirinsa garau yake, har da zai ce ya rabu da zunubinsa?

10. Allah yana ƙin masu ma'aunin algus.

11. Ayyukan da saurayi yake yi suke bayyana yadda yake, kana iya sani ko shi amintacce ne, mai nagarta.

12. Ubangiji ya ba mu ido don mu gani, ya ba mu kunne don mu ji.

13. Idan barci ne sana'arka za ka talauce. Ka yi ta aiki za ka sami wadataccen abinci.

14. Mai saye yakan yi kukan tsada a kullum, amma yakan tafi ya yi ta fāriya a kan ya iya ciniki.

15. In ka san abin da kake faɗa, kana da wani abu wanda ya fi zinariya da lu'ulu'ai tamani.