Littafi Mai Tsarki

K. Mag 20:21-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, amfaninta kaɗan ne.

22. Kada ka ɗaukar wa kanka fansa, ka dogara ga Ubangiji shi zai yi sakamako.

23. Ubangiji yana ƙin waɗanda suke awo da ma'aunin algus.

24. Ubangiji ya ƙayyade hanyoyinmu, ta ƙaƙa wani zai ce ya fahimci rai?

25. Ka yi tunani a hankali kafin ka yi wa'adi za ka miƙa wa Allah wani abu, mai yiwuwa ne ka yi da na sani nan gaba.

26. Sarki mai hikima zai bincika ya gane waɗanda suke aikata mugunta, ya hukunta su ba tausayi.

27. Ubangiji ne ya ba mu hankali da lamiri, ba za mu iya ɓoye masa ba.

28. Sarki zai zauna dafa'an cikin mulkinsa muddin yana mulki da aminci, da adalci, da daidaita.

29. Ƙarfin samari abin darajantawa ne, furfurar tsofaffi abar girmamawa ce.

30. Wani lokaci sai mun sha wuya muke sāke hanyoyinmu.