Littafi Mai Tsarki

K. Mag 20:2-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ka ji tsoron fushin sarki kamar yadda za ka ji tsoron zaki mai ruri, sa shi ya yi fushi kashe kai ne.

3. Kowane wawa yakan fara yin jayayya, abin da ya fi daraja shi ne ka fita ka ware kanka.

4. Manomin da ya cika lalaci, ya kasa nome gonakinsa a kan kari, a lokacin girbi ba zai sami kome ba.

5. Tunanin mutum kamar ruwa yake a rijiya mai zurfi, sai mai basira ya iya ya jawo shi.

6. Kowa gani yake shi mai biyayya ne, mai aminci. Amma ina? Ko ka yi ƙoƙari ka sami amintacce ɗaya daga cikinsu, ba za ka samu ba.

7. 'Ya'yan da mahaifinsu amintacce ne, wanda yake aikata abin da yake daidai, sun yi sa'a.

8. Sarkin da yake yin shari'a ta gaskiya, da ganin mugunta ya san ta.

9. Wane ne zai iya cewa lamirinsa garau yake, har da zai ce ya rabu da zunubinsa?

10. Allah yana ƙin masu ma'aunin algus.

11. Ayyukan da saurayi yake yi suke bayyana yadda yake, kana iya sani ko shi amintacce ne, mai nagarta.

12. Ubangiji ya ba mu ido don mu gani, ya ba mu kunne don mu ji.

13. Idan barci ne sana'arka za ka talauce. Ka yi ta aiki za ka sami wadataccen abinci.

14. Mai saye yakan yi kukan tsada a kullum, amma yakan tafi ya yi ta fāriya a kan ya iya ciniki.

15. In ka san abin da kake faɗa, kana da wani abu wanda ya fi zinariya da lu'ulu'ai tamani.

16. Sai wawa kaɗai yake ɗaukar lamunin biyan basusuwan da baƙo ya ci, ya kamata a karɓi dukiyarsa jingina.

17. Abin da ka samu ta hanyar zamba kakan ji daɗinsa kamar abinci mai kyau, amma ko ba jima ko ba daɗe zai zama kamar yashi cike da bakinka.

18. Ka nemi kyakkyawar shawara za ka yi nasara, kada ka jefa kanka cikin yaƙi ba tare da shiri ba.

19. Mai baza jita-jita ba shi da asiri, ka yi nesa da mai yawan surutu.

20. Idan ka zagi iyayenka, za ka mutu kamar fitilar da ta mutu cikin duhu.