Littafi Mai Tsarki

K. Mag 20:17-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Abin da ka samu ta hanyar zamba kakan ji daɗinsa kamar abinci mai kyau, amma ko ba jima ko ba daɗe zai zama kamar yashi cike da bakinka.

18. Ka nemi kyakkyawar shawara za ka yi nasara, kada ka jefa kanka cikin yaƙi ba tare da shiri ba.

19. Mai baza jita-jita ba shi da asiri, ka yi nesa da mai yawan surutu.

20. Idan ka zagi iyayenka, za ka mutu kamar fitilar da ta mutu cikin duhu.

21. Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, amfaninta kaɗan ne.

22. Kada ka ɗaukar wa kanka fansa, ka dogara ga Ubangiji shi zai yi sakamako.

23. Ubangiji yana ƙin waɗanda suke awo da ma'aunin algus.

24. Ubangiji ya ƙayyade hanyoyinmu, ta ƙaƙa wani zai ce ya fahimci rai?

25. Ka yi tunani a hankali kafin ka yi wa'adi za ka miƙa wa Allah wani abu, mai yiwuwa ne ka yi da na sani nan gaba.

26. Sarki mai hikima zai bincika ya gane waɗanda suke aikata mugunta, ya hukunta su ba tausayi.

27. Ubangiji ne ya ba mu hankali da lamiri, ba za mu iya ɓoye masa ba.

28. Sarki zai zauna dafa'an cikin mulkinsa muddin yana mulki da aminci, da adalci, da daidaita.

29. Ƙarfin samari abin darajantawa ne, furfurar tsofaffi abar girmamawa ce.

30. Wani lokaci sai mun sha wuya muke sāke hanyoyinmu.