Littafi Mai Tsarki

K. Mag 20:10-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Allah yana ƙin masu ma'aunin algus.

11. Ayyukan da saurayi yake yi suke bayyana yadda yake, kana iya sani ko shi amintacce ne, mai nagarta.

12. Ubangiji ya ba mu ido don mu gani, ya ba mu kunne don mu ji.