Littafi Mai Tsarki

K. Mag 2:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ɗana, ka koyi abin da nake koya maka, sam kada ka manta da abin da na faɗa maka ka yi.

2. Ka kasa kunne ga abin da yake na hikima, ka yi ƙoƙari ka fahimce shi.

3. I, ka roƙi ilimi da tsinkaya.

4. Ka nema da iyakar ƙoƙarinka kamar yadda za ka nemi azurfa, ko kowace irin ɓoyayyiyar dukiya.

5. Idan ka yi za ka san abin da ake nufi da tsoron Ubangiji. Za ka yi nasara a kan koyon sanin Allah.

6. Ubangiji ne yake ba da hikima. Ilimi da fahimi kuwa suna cikin kalmominsa.

7. Shi yake tanada wa adalai taimako da kiyayewa, wato mutane masu aminci.

8. Yakan kiyaye waɗanda suke lura da kyau, ya kiyaye waɗanda suke dogara gare shi.

9. Idan ka kasa kunne gare ni za ka san abin da yake daidai, da abin da yake gaskiya, da abin da yake na kirki. Za ka san abin da za ka yi.