Littafi Mai Tsarki

K. Mag 17:7-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Mutumin da yake kamili ba ya faɗar ƙarya, haka ma wawa ba zai faɗi wani abin kirki ba.

8. Waɗansu mutane suna tsammani cin rashawa yakan yi aiki kamar sihiri, sun gaskata zai iya yin kome.

9. Idan kana so mutane su so ka, ka riƙa yafe musu sa'ad da suka yi maka laifi. Mita takan raba abuta.