Littafi Mai Tsarki

K. Mag 12:25-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Damuwa takan hana wa mutum farin ciki, amma kalmomin alheri za su sa shi ya yi murna.

26. A ko yaushe adalin mutum yakan gwada halinsa, amma mugaye sukan ɓata a hanya.

27. Rago ba zai kai ga biyan bukatarsa ba, amma mai ƙwazo zai sami dukiya.

28. Adalci hanyar rai ne, amma wauta hanyar mutuwa ce.