Littafi Mai Tsarki

K. Mag 12:18-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Maganganun rashin tunani suke sa rauni mai zurfi kamar saran takobi, amma kalmomin mai hikima sukan warkar da raunuka.

19. Gaskiya dawwamammiya ce, amma ƙarya ƙurarriya ce.

20. Waɗanda suke shawarta mugunta za a auka musu farat ɗaya, amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.

21. Ba wani mugun abu da zai sami adali, amma mugaye ba za su sami kome ba, sai wahala.

22. Ubangiji yana ƙin maƙaryata, amma yana murna da masu faɗa da cikawa.

23. Mai la'akari zai bar wa cikinsa abin da ya sani, amma wawaye sukan yi ta tallar wautarsu.

24. Mutum mai mai da hankali ga aikinsa zai sami iko, amma ragwanci zai sa mutum ya zama bawa.

25. Damuwa takan hana wa mutum farin ciki, amma kalmomin alheri za su sa shi ya yi murna.

26. A ko yaushe adalin mutum yakan gwada halinsa, amma mugaye sukan ɓata a hanya.

27. Rago ba zai kai ga biyan bukatarsa ba, amma mai ƙwazo zai sami dukiya.