Littafi Mai Tsarki

K. Mag 12:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Sakayyar mutum ta rataya ne a kan maganarsa da aikinsa, zai sami abin da ya cancance shi.

15. Wawa a kullum tsammani yake abin da yake yi daidai ne, amma masu hikima sukan kasa kunne ga shawara.

16. Sa'ad da wawa ya hasala, nan da nan kowa zai sani, amma mai la'akari ba zai nuna ya kula ba.

17. Sa'ad da ka faɗi gaskiya, ka yi adalci, amma ƙarairayi su ne jagorar aikata rashin adalci.

18. Maganganun rashin tunani suke sa rauni mai zurfi kamar saran takobi, amma kalmomin mai hikima sukan warkar da raunuka.

19. Gaskiya dawwamammiya ce, amma ƙarya ƙurarriya ce.

20. Waɗanda suke shawarta mugunta za a auka musu farat ɗaya, amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.