Littafi Mai Tsarki

K. Mag 12:13-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Maganganun mugun sukan zamar masa tarko, amma amintacce yakan fid da kansa daga cikin wahala.

14. Sakayyar mutum ta rataya ne a kan maganarsa da aikinsa, zai sami abin da ya cancance shi.

15. Wawa a kullum tsammani yake abin da yake yi daidai ne, amma masu hikima sukan kasa kunne ga shawara.