Littafi Mai Tsarki

K. Mag 12:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Mutumin da yake ƙaunar ilimi yakan so a faɗa masa kuskurensa, wauta ce mutum ya ƙi yarda a faɗa masa laifinsa.

2. Ubangiji yana murna da mutanen kirki, amma yakan hukunta masu shirya mugunta.

3. Mugunta ba ta kawo zaman lafiya, amma adalai sukan tsaya daram.

4. Matar kirki abar fāriya ce, abar murna ga mijinta, amma idan ta sa shi kunya, ta zama masa kamar ciwo a ƙashinsa.

5. Amintattun mutane za su yi maka abin da yake daidai, amma mugaye za su ruɗe ka.

6. Maganganun mugaye na kisankai ne, amma kalmomin adalai sukan ceci waɗanda ake neman ransu.

7. Mugaye sukan gamu da faɗuwarsu, ba magāda, amma iyalan adalai sukan dawwama.

8. Idan kai haziƙi ne, za a yabe ka, amma idan kai dakiki ne, mutane za su raina ka.

9. Gara kana talakanka, kana neman abinci, da ka mai da kanka kai wani abu ne, alhali kuwa abin da za ka ci ya fi ƙarfinka.

10. Mutumin kirki yakan lura da dabbobinsa, amma mugaye sukan yi wa nasu ƙeta.

11. Manomin da yake aiki ƙwarai yana da isasshen abinci. Wauta ce a ɓatar da lokaci a kan aikin banza.

12. Iyakar abin da mugaye suke so, shi ne su sami muguntar da za su yi, amma adalai suna tsaye daram.

13. Maganganun mugun sukan zamar masa tarko, amma amintacce yakan fid da kansa daga cikin wahala.

14. Sakayyar mutum ta rataya ne a kan maganarsa da aikinsa, zai sami abin da ya cancance shi.

15. Wawa a kullum tsammani yake abin da yake yi daidai ne, amma masu hikima sukan kasa kunne ga shawara.

16. Sa'ad da wawa ya hasala, nan da nan kowa zai sani, amma mai la'akari ba zai nuna ya kula ba.