Littafi Mai Tsarki

K. Mag 11:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji yana ƙin masu yin awo da ma'aunin zamba, amma yana farin ciki da masu yin awo da ma'auni na gaskiya.

2. Masu girmankai za a kunyatar da su nan da nan. Hikima ce mutum ya zama mai kamewa.

3. Mutanen kirki su ne gaskiya takan bi da su. Rashin aminci kuwa yana hallaka maciya amana.

4. Dukiya ba ta da wani amfani a ranar mutuwa, amma adalci zai hana ka mutuwa.

5. Gaskiya takan sa zaman mutanen kirki ya zama a sawwaƙe, amma mugun mutum shi yake kā da kansa da kansa.

6. Adalci yakan ceci amintaccen mutum, amma marar aminci, haɗamarsa ce take zamar masa tarko.

7. Mugun mutum yakan mutu da burinsa. Dogara ga dukiya bai amfana kome ba.

8. Akan kiyaye adali daga wahala, amma takan auko wa mugu.

9. Mutane sukan sha hasara ta wurin maganar marasa tsoron Allah, amma hikimar adalai takan yi ceto.

10. Birni yakan yi farin ciki saboda wadatar mutanen kirki, akwai kuma sowa ta farin ciki sa'ad da mugaye suka mutu.

11. Biranen da adalai suke cikinsu sukan ƙasaita, amma maganganun mugaye sukan hallakar da su.

12. Wauta ce a yi wa waɗansu maganar raini, amma mutum mai la'akari yakan kame bakinsa.