Littafi Mai Tsarki

K. Mag 10:16-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Sakayyar da za a yi wa mutumin kirki ta rai ce, amma zunubi yakan sa a ƙara yin wani zunubi.

17. Mutumin da yake kasa kunne sa'ad da ake kwaɓarsa zai rayu, amma duk wanda bai yarda da kuskurensa ba yana cikin hatsari.

18. Mutumin da yake faɗar ƙarairayi maƙiyi ne, dukan wanda yake baza jitajita wawa ne.

19. Bisa ga yawan surutunka, mai yiwuwa ne ƙwarai ka yi zunubi, amma idan kai mai la'akari ne, sai ka yi shiru.

20. Kalmomin mutumin kirki suna kama da azurfa tsantsa, amma shawarwarin mugu ba su da wani amfani.