Littafi Mai Tsarki

Fit 6:26-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Wannan Haruna ne da Musa, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana su fito da Isra'ilawa daga cikin ƙasar Masar, ƙungiya ƙungiya.

27. Su ne waɗanda suka yi magana da Sarkin Masar ya bar Isra'ilawa su fita daga Masar. Musa da Haruna ne suka yi wannan.

28. Wata rana Ubangiji ya yi magana da Musa a ƙasar Masar ya ce,

29. “Ni ne Ubangiji, sai ka faɗa wa Fir'auna, Sarkin Masar, dukan abin da na faɗa maka.”

30. Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, yaya Fir'auna zai kasa kunne gare ni?”