Littafi Mai Tsarki

Fit 5:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Manyan Isra'ilawa kuwa suka tafi suka yi kuka a gaban Fir'auna, suka ce, “Me ya sa ka yi wa bayinka haka?

16. Ba a ba mu budu, amma ana ce mana mu yi tubali. Ga shi ma, dūkan bayinka suke yi. Ai, jama'arka ne suke da laifin.”

17. Fir'auna kuwa ya ce musu, “Ku ragwaye ne ƙwarai, shi ya sa kuke cewa a bar ku ku tafi, ku miƙa wa Ubangiji hadaya.

18. Ku tafi, ku kama aiki, ba za a ba ku budu ba, duk da haka za ku cika yawan tubali da aka sa muku.”

19. Manyan Isra'ilawa suka ga lalle sun shiga uku, da yake aka ce dole su cika yawan tubali da aka yanka musu kowace rana.

20. Da suka fita daga gaban Fir'auna, sai suka sadu da Musa da Haruna, suna jiransu.

21. Suka ce wa Musa da Haruna, “Allah ya duba, ya hukunta ku, gama kun sa mun yi baƙin jini a wurin Fir'auna da barorinsa, har suka ɗauki takobi don su kashe mu.”