Littafi Mai Tsarki

Fit 25:4-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. da ulu mai launin shuɗi, da mai launin shunayya, da mai launin ja, da lilin mai laushi, da gashin akuya,

5. da jemammun fatun raguna, da fatun awaki, da itacen ƙirya,

6. da mai domin fitila, da kayan yaji domin man keɓewa, da turaren ƙonawa,

7. da onis, da duwatsun da za a mammanne a falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

8. Za su yi tsattsarkan wuri domina, don in zauna tare da su.

9. Za ku yi mazaunina da kayayyakinsa duka, bisa ga irin fasalin da zan nuna maka.”

10. “Sai ku yi akwatin alkawari da itacen maje, tsawonsa ya zama kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa ya zama kamu ɗaya da rabi.

11. Ku dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje. Ku yi wa gyaffansa ado da gurun zinariya.

12. Za ku yi wa akwatin ƙawanya huɗu na zinariya ku liƙa a kowace kusurwar akwatin, wato ƙawanya biyu a kowane gefe na tsawon.

13. Za ku kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya.