Littafi Mai Tsarki

Fit 25:2-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Faɗa wa Isra'ilawa su karɓo mini kaya daga dukan wanda ya yi niyyar bayarwa.

3. Ga irin sadakokin da za ku karɓa, zinariya, da azurfa, da tagulla,

4. da ulu mai launin shuɗi, da mai launin shunayya, da mai launin ja, da lilin mai laushi, da gashin akuya,

5. da jemammun fatun raguna, da fatun awaki, da itacen ƙirya,