Littafi Mai Tsarki

Fit 25:16-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. A kuma sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka a cikin akwatin.

17. “Za ku yi wa akwatin murfi da zinariya tsantsa, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

18. Za ku yi siffofin kerubobi biyu da ƙerarriyar zinariya, ku sa a gefen nan biyu na murfin.

19. Siffar kerub ɗaya a kowane gefe. Ku yi su ta yadda za su zama ɗaya da murfin.

20. Fikafikan kerubobin za su miƙe bisa domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin.

21. Za ku sa murfin bisa akwatin. A cikin akwatin kuwa za ku sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka.

22. A nan zan zo in sadu da kai, in yi magana da kai, wato tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari. Zan ba ka umarnaina duka don Isra'ilawa.”

23. “Ku yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

24. Ku dalaye shi da zinariya tsantsa, ku kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya.