Littafi Mai Tsarki

Fit 12:49-51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

49. Wannan ka'ida ta shafi ɗan ƙasa daidai da baƙon da yake baƙunci tsakaninku.”

50. Isra'ilawa suka yi na'am da shi, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.

51. A wannan rana ce Ubangiji ya fitar da Isra'ilawa runduna runduna daga ƙasar Masar.