Littafi Mai Tsarki

Ayu 8:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Bildad ya yi magana.

2. “Ka gama maganganunka marasa kan gado duka?

3. Allah bai taɓa yin danniya ba,Bai kuma taɓa fāsa aikata abin da yake daidai ba.

4. Lalle 'ya'yanka sun yi wa Allah zunubi,Don haka ya hukunta su yadda ya cancanta.

5. Amma sai ka juyo ka yi roƙo ga Allah Maɗaukaki.

6. Idan kana da tsarki da aminci, Allah zai taimake ka,Ya maido da iyalin gidanka, ya yi maka sakayya.