Littafi Mai Tsarki

Ayu 6:3-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Da sun fi yashin teku nauyi.Kada ka yi mamaki da maganganun da nake yi.

4. Allah Maɗaukaki ya harbe ni da kibau,Dafinsu kuwa ya ratsa jikina.Allah ya jera mini abubuwa masu banrazana.

5. “Idan jaki ya sami ciyawar ci, muradinsa ya biya,In ka ji saniya ta yi shiru, tana cin ingirici ne.

6. Amma wane ne zai iya cin abinci ba gishiri?Akwai daɗin ɗanɗano ga farin ruwan ƙwai?

7. Ba na jin marmarin cin abinci irin haka,Kowane irin abu da na ci yakan sa mini cuta.