Littafi Mai Tsarki

Ayu 6:25-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Kila muhawara mai ma'ana ta rinjaye ni,Amma yanzu duk maganar shirme kuke yi.

26. Kuna so ku amsa maganganuna?Don me?Mutumin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi,Ba wata maganar da zai yi in ba shirme ba.

27. Kukan jefa wa bayi da marayu kuri'a,Kukan arzuta kanku daga abokanku na kurkusa.

28. Ku dubi fuskata,Lalle ba zan faɗi ƙarya ba.

29. Kai, kun zaƙe, ku daina aikata rashin adalci,Kada ku sa mini laifi, nake da gaskiya.

30. Amma duk da haka kuna tsammani ƙarya nake yi.Kuna tsammani ba zan iya rarrabe tsakanin gaskiya da ƙarya ba.”