Littafi Mai Tsarki

Ayu 6:13-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ba ni da sauran ƙarfi da zan ceci kaina,Ba inda zan juya in nemi taimako.

14. “A cikin irin wannan wahalaIna bukatar amintattun abokai,Ko da na rabu da Allah, ko ina tare da shi.

15. Amma ku abokaina,kun ruɗe ni,Kamar rafi wanda yakan ƙafe da rani.

16-17. Rafin yana cike da iska mai laima da ƙanƙara,Amma lokacin zafi sai su ɓace,Kwacciyar rafin, sai ta bushe ba kome.

18. Ayari sukan ɓata garin neman ruwa,Su yi ta gilo, har su marmace a hamada.

19. Ayari daga Sheba da Tema suka yi ta nema,

20. Amma sa zuciyarsu ta ƙare a gefen busassun rafuffuka,

21. Kamar rafuffukan nan kuke a gare ni,Kun ga abin da ya same ni, kun gigita.

22. Na roƙe ku ku ba ni kyauta ne?Ko kuwa na roƙe ku ku ba wani rashawa domina?

23. Ko kuma na roƙe ku ku cece ni daga maƙiyi ko azzalumi ne?

24. “To, sai ku koya mini, ku bayyana mini laifofina,Zan yi shiru in kasa kunne gare ku.

25. Kila muhawara mai ma'ana ta rinjaye ni,Amma yanzu duk maganar shirme kuke yi.

26. Kuna so ku amsa maganganuna?Don me?Mutumin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi,Ba wata maganar da zai yi in ba shirme ba.