Littafi Mai Tsarki

Ayu 6:10-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Da na san zai yi haka, da sai in yi tsalle don murna,Da ba zan kula da tsananin azabar da nake ciki ba.Ban taɓa yin gāba da umarnan Allah ba.

11. Wane ƙarfi ne nake da shi na rayuwa?Wane sa zuciya kuma nake da ita,tun da na tabbata mutuwa zan yi?

12. Da dutse aka yi ni?Ko da tagulla aka yi jikina?

13. Ba ni da sauran ƙarfi da zan ceci kaina,Ba inda zan juya in nemi taimako.

14. “A cikin irin wannan wahalaIna bukatar amintattun abokai,Ko da na rabu da Allah, ko ina tare da shi.

15. Amma ku abokaina,kun ruɗe ni,Kamar rafi wanda yakan ƙafe da rani.