Littafi Mai Tsarki

Ayu 5:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Na ga waɗansu wawaye waɗanda ake gani kamar suna zaune lafiya,Amma nan da nan sai na la'anci gidajensu.

4. Ko kaɗan, 'ya'yansu maza ba za su taɓa zama lafiya ba.Ba wanda zai tsaya musu a ɗakin shari'a.

5. Mayunwata za su ci amfanin gonar wawa,Har da hatsin da yake girma cikin ƙayayuwa,Waɗanda suke jin ƙishirwa za su ji ƙyashin dukiyarsa.

6. Zunubi ba ya tsirowa daga ƙasa,Haka ma wahala ba ta tsirowa daga ƙasa.

7. Ai, an haifi mutum domin wahala ne,Tabbatacce ne kamar yadda tartsatsin wuta suke tashi.

8. “In da ni ne kai, da sai in juya wurin Allah,In kai ƙarata a wurinsa.